Shirye-shiryen Diplomar Shari'ar Musulunci

An buɗu yin rigistar rukuni na biyu, na Diplomar
ilumimmukan Shari’ar Musulunci.

Siffantawa

tsarin karatu ne na Diploma, na tsawon shekara ɗaya. an raba karatun zuwa rukuni-rukuni, za a sanar da ɗaukar ɗalibai a kowane rukuni, a Tasahar Africa tv3, da kuma dandulansu na sa da zumunta tun kafin fara rijista da cikakken lokaci. Wannan Diplomar tana da zango biyu, da ɗalibi zai karanci maddoji shida a cikinsu a kowane zangon. bayan ɗalibi ya ci jarrabawar ƙarshe a kowane zango, to zai sami takardar shadar kammalawa ta Diplomar Shari’ar Musulunci, daga Tsangayar Africa.

Bayani game da manhajar karatu

Za a gabatar da manhajar ne ta hanyar

Litattafai na PDF

Sanya karatu kai tsaye a YouTube

Laccoci na sauraro (Mp3)

Laccoci na bidiyo waɗanda za a gani a tashar Africa tv3

Tsarin karatu

tsarin karatun ana yin shi ne daga nesa, ta yadda ɗalibi zai zaɓi tsarin karatun da zai dace da shi, daga cikin mabambantan tsaruka, kamar yanayin tsarin yadda ake gabatar da maddojin ta mabambantan hanyoyi, ta hanyar littafin karatu, da laccoci na bidiyo, da kuma na sauti.

ka sauke littafin jagoran ɗalibi, domin sanin komai game da tsarin karatu a wannan dandalin

Malaman da za su koyar

Dr. Abdulƙadir Isma_il

Dr. Abubakar M. Birnin-Kudu

Shkh. AbdulMuɗɗalib Awwal Gusau

Dr. Nazifi Inuwa

Dr. Yusha_u Hanafi

Dr. Habeeb Tijjani Tahir

Shkh. AbdulMuɗɗalib Awwal Gusau