Tsangayar Africa

Shafin tsangayar Africa na internet na koyar da ilumummukan shari’a a kyauta.

tsangayar Africa tsangayace shakundum ta koyarwa ta hanyar interne, An samar da Tsangayar Africa ne da nufin taimaka wa al’umar Africa, wajen samun ingantacciyar fahimtar Musulunci, ta hanyar Ƙur’ani Mai girma, da Sunnar Annabi ﷺ.
Dandali ne shakundum wanda ke gabatar da shirin ilimantarwa da nufin kusantar da ilimi zuwa ga masu sha’awar shi, ta hanyar Internet, da kafofin sada zumunta, da kuma kan akwatin talabijin na Africa tv3. 

Shirye-shiryen Tsangayar Africa

Shirye-shiryen Diplomar Shari'ar Musulunci.

tsarin karatu ne na Diploma, na tsawon shekara ɗaya. an raba karatun zuwa rukuni-rukuni, za a sanar da ɗaukar ɗalibai a kowane rukuni, a Tasahar Africa tv3, da kuma dandulansu na sa da zumunta tun kafin fara rijista da cikakken lokaci. Wannan Diplomar tana da zango biyu, da ɗalibi zai karanci maddoji shida a cikinsu a kowane zangon. bayan ɗalibi ya ci jarrabawar ƙarshe a kowane zango, to zai sami takardar shadar kammalawa ta Diplomar Shari’ar Musulunci, daga Tsangayar Africa.

Tsarin karatu

tsarin karatun ana yin shi ne daga nesa, ta yadda ɗalibi zai zaɓi tsarin karatun da zai dace da shi, daga cikin mabambantan tsaruka, kamar yanayin tsarin yadda ake gabatar da maddojin ta mabambantan hanyoyi, ta hanyar littafin karatu, da laccoci na bidiyo, da kuma na sauti.

ka sauke littafin jagoran ɗalibi, domin sanin komai game da tsarin karatu a wannan dandalin

abarai na ƙarshe

Muna yi maku albishir da cewa yanzu zaku iya yin rijista a Diplomar ilimin Shari’ar Musulunci ta Tsangyar Africa a kyauta

Domin neman ƙari

Za a gabatar da manhajar ne ta hanyar

Litattafai na PDF

Sanya karatu kai tsaye a YouTube

Laccoci na sauraro (Mp3)

Laccoci na bidiyo waɗanda za a gani a tashar Africa tv3

Bayani game da manhajar karatu

Malaman da za su koyar

Dr. Yusha_u Hanafi

Dr. Habeeb Tijjani Tahir

Shkh. Alkali Murtadha Al-Misry

Dr. Abdulƙadir Isma_il

Dr. Abubakar M. Birnin-Kudu

Shkh. AbdulMuɗɗalib Awwal Gusau

Dr. Nazifi Inuwa

Ƴan gajerun kwasakwasai masu buɗaɗɗen lokaci

Akwai wasu kwasakwasai gajeru na Shari’ar Musulunci, waɗanda za a ɗauki wani batu, ko wasu batuttukan da ya wajaba musulmi ya san su. A koyaushe za su zama a buɗe, ta yadda ɗalibi zai iya yin rigista a duk sanda yake so, kuma ya yi karatun a lokacin da ya dace da shi, bayan ya gama kwas ɗin, kuma ya ci jarrabawa, zai sami takardar shaidar kammala kwas ɗin.

kididdiga

Idadi ya wanafunzi waliosajiliwa

20000

Idadi ya wanafunzi waliohitimu

20000

Wanaofwata mitandao ya kijamii

20000

Habari za hivi karibuni