Bayan kammala wannan shirin, ana sa ran a sami sakamako kamar haka:
Ɗalibai su fahimci abin da suke da buƙatuwa zuwa gare shi na ilimin shari’a daga tushe, wanda ba yadda za a iya bauta wa Allah sai da shi.
Ɗalibi ya sami mafi girman amfani, wato ya bauta wa Allah a bisa ilimi.
Ɗalibi ya ba da gudunmawa wajen karantar da mutanen gidansa, da makusantansa abin da suke da buƙata na lamarin addininsu, ba tare da ɓangaranci, ko wuce-gona-da-iri ba, tare da sanar da su abin da zai sanya su siffantuwa da hali na ƙwarai.
Ɗalibi ya samu ya ci gaba da zarar ya ƙaunaci wannan ilimin, ya kuma dinga ƙarin neman ilimi, da bincike, har ya sami damar shiga fagen ƙira zuwa ga addinin Allah, da kuma fagen yin hidima ga ilimi, kamar yin bincike a ilimin Shari’a, ko kuma bitar ilimi, ko wallafa binciken ilimi, da kuma tsara darusa, da huɗubobi, da laccoci.
Wannan shirin zai taimaka wa ɗalibi da yadda zai bayar da karatu, cikin abin da ya iya na mas’alolin ilimi a masallatai, da guraren jama’a, ko ta hanyar internet, kamar yin rubutu, da yaɗa batutuwa na shari’ar musulunci.
Allah Ya cika mana burinmu, Shi ne Mai shiryarwa zuwa ga hanyar shiriya.