Jawabin shugaba

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Salati da aminci su ƙara tabbata ga mai  koyar da mutane alheri, Annabinmu Muhammad ﷺ da iyalan gidansa, da Sahabbansa bakiɗaya, bayan haka.

Haƙiƙa ilimin shari’a shi ne hanyar dake sadarwa zuwa ga yardar Allah, da kuma samun babban matsayi a aljanna, shi ne ke isarwa zuwa ga dukkanin alheran duniya da lahira, kuma shi ne ke gyara mutum da kuma sauran al’umma, da shi ne al’umma take samun girma, da jagoranci, mafi girman kamben da Malamai suke da shi; shi ne faɗin Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce: 

{شَهِدَ اللّهُ أَنَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ وَالْمَلاَئِكَةُ وَأُوْلُواْ الْعِلْمِ قَآئِمَاً بِالْقِسْطِ} [آل عمران: 18

{Allah ya sheda cewa: Lalle ne babu abin bautawa bisa cancanta face shi, haka ma Mala’iku da Ma’abota ilimi, alhali yana tsaye a kan adalci} [Ali Imran: 17].

Saboda girman lamarin ilimi ne; Allah Ya umarci ManzonSa ﷺ da neman ƙarin ilimi. Allah ﷻ Ya ce:

{وقل ربي زدني علما}

{kuma ka ce ya Ubangiji Ka ƙara mini ilimi} [Suratu: Ɗaha: 114]. 

Nassoshi masu ya wa sun zo waɗanda suke nuni zuwa ga falalar ilimi, da ma’abotansa, -Manzon Allah ﷺ – ya ce: “Duk wanda ya bi wata hanya yana mai neman ilimi a cikinta, Allah zai sauƙaƙe masa hanya zuwa Aljanna da shi”. Muslim ne ya ruwaito shi.

Domin haka (Tsangayar Africa) ta zo a matsayin makaranta ta Internet ta farko, wacce take koyar da al’umar Africa waɗanda ke magana da harasan da ba na Larabci ba, kuma ta zo domin ta biya buƙatar musulmai ta koyon ilimin Shari’ar Musulunci a Africa, da harasa mabambanta, domin kuma ta sauƙaƙa neman ilimi ta hanyar internet ga wanda yake da lokaci da wanda ma ba shi da lokaci.

Shirin Tsangayar Africa yana nufin koyar da ilimin Shari’ar Musulunci, wanda aka ciro shi daga littafin Allah da ingantacciyar Sunnar ManzonSa ﷺ, a kan fahimtar magabata na ƙwarai, da kuma Aƙidarsu,  an tsara wannan manhaji ne ta hanyar tattara abin da ya dace da ɗalibai, da kuma bi daki-daki da kuma sauƙaƙawa, da kuma gamewa, wanda musulmi yake buƙata domin ya fahimci addininsa, tare da nisantar faɗaɗa bayani, da ambaton saɓanin Fiƙihu, sannan an tsara littafin da kyakyawan bugu, domin ya ba wa ɗalibi damar karatu, ta hanyar da ta dace da zamani, da ci gabansa ta ɓangaren koyo da koyarwa.

Ina roƙon Allah maɗaukakin Sarki, Ya datar da kowa, Ya amfanar da kowa da wannan abin da Tsangayar Africa take gabatarwa, kuma ina roƙon Shi Maɗaukakin Sarki Ya sanya dominSa aka yi Kuma Ya karɓa. 

Shugaban Tsangayar Africa, 

Dr. Habeeb Tijjani Tahir