An samar da Tsangayar Africa ne da nufin taimaka wa al’umar Africa, wajen samun ingantacciyar fahimtar Musulunci, ta hanyar Ƙur’ani Mai Girma, da Sunnar Annabi ﷺ.
Dandali ne shakundum wanda ke gabatar da shirin ilimantarwa da nufin kusantar da ilimi zuwa ga masu sha’awar shi, ta hanyar Internet, da kafofin sada zumunta, da kuma kan akwatin talabijin na Africa tv3.
Dandalin ya dogara da samar da ilimi mai zurfi akan tsarin: Massive Open Online Course wanda ake taƙaita shi da kalmar (MOOCs) Tsangayar tana aiki ne 100%
ta Internet inda ɗalibai za su iya shiga darussa ta hanyar kwamfuta da na’urori masu ƙwaƙwalwa, kuma suna iya halartar bitoci ta hanyar darussan da aka ɗauke su ta hanyar bidiyo da kuma littattafan amfanin na’ura mai ƙwaƙwalwa, da kuma amsa tambayoyin auna fahimta.
Kuma ta dogara da fitattun malamai masu wa’azi na Ahlus Sunna Wal Jama’a masu magana da harshen Hausa.
Muna burin mutum dubu goma su shiga wannan tsarin a zango ukun farko.
Tsangayar Africa ta zamanto jagora a fagen koyarwa da harshen Hausa ta hanyar Internet, da hanyoyi na zamani, da kuma kafafen da suke da dangantaka da Tsangayar Africa, da sauran shafukan Internet mabambanta.

An kiyaye duk haƙƙoƙin mallaka © 2024