Shafin sharuɗan yin rijista:

  • Tsangayar Africa ta koyar da ilimi daga nesa: Na farin cikin karɓar dukkanin ɗalibai; masu sha’awar koyon ilimin Shari’ar Musulunci, ba tare da buƙatar samun wata takardar shaida ta musamman ba.
  • Kawai abin da ake buƙata shi ne ya kasance ya iya harshen Hausa, ta hanyar yin magana, da rubutu, da karatu, saboda shi ne harshen da ake amfani da shi a Tsangayar Africa, wajen koyo da koyarwa.
  • Kuma kada shekarun ɗalibi su yi ƙasa da shekara 15.
  • Sannan kuma ɗalibi ya yi rijista ta yadda aka buƙata.
تبقى لفتح التسجيل في الدفعة الأولى​
يوم
ساعة
دقيقة
ثانية