Ana koyar da Diplomar Shari’a a Tsangayar Afirka ta hanyar tsarin kwasa-kwasai inda ake koyar da kwasa-kwasan a jere, inda dalibai za su yi karatun madda ɗaya har zuwa yakammala ta, kuma ya yi jarrabawarta, sannan ya ci gaba da karatun madda ta gaba
Litattafai na PDF
Laccoci na bidiyo waɗanda za a gani a tashar Africa tv3
Laccoci na sauraro (Mp3)
Sanya karatu kai tsaye a YouTube
Ɗalibi zai iya sauke litattafan karatu kyuata, a shafinmu na internet, kuma ɗalibi zai iya bibiyar lacca kai-tsaye, ta tashar Africa Tv3 a kullum, sannan kuma akwai jarrabawar wata wata, da ta sati sati. Kuma Tsangayar Africa tana tsara wa kowacce madda zama na kai-tsaye tare da malamai ta hanyar Facebook, a kowanne wata sau ɗaya.
Ita ce jarrabawar da ɗalibai suke yi waɗanda ba su sami makin da zai ba su damar cin jarrabawa ba a jarrabawa ta asali, ko kuma ba su sami damar yin jarrabawar asali ba.
Ana bayar da damar yin su bakiɗaya a lokaci guda bayan kammala zangon karatun jarrabawar cike gurbi ta dukkan maddojin.
Kuma ana ba ta tsawon tazarar kwana goma ne kawai.
An kiyaye duk haƙƙoƙin mallaka © 2023