Hanyar yin karatu
  • Tsarin Tsangayar Africa yana gudanar da abubuwan da ake buƙata, domin tabbatuwar koyarwa, ta hanyar sanya manhajar karatu a rubuce, da kuma bidiyon da zai taimak wajen fahimtar karatun, da kuma yin jarrabawa a kullum, da kuma ta sati sati, da ta wata wata, da kuma jarrabawar ƙarshe, da kuma bibiyar ɗalibai, da kuma samun cikakkiyar sadarwa a tsakanin ɗalibai, da malamai.

Laccoci na bidiyo waɗanda za a gani a tashar Africa tv3

Laccoci na sauraro (Mp3)

Litattafai na PDF

Matangazo ya moja kwa moja kwenye YouTube

Tsawon lokacin da za a ɗauka ana karatun Diplomar:
  • Tsarin karatun Diploma ɗin na tsangayar Africa an kasa shi zuwa zangunan karatu biyu, kowane zango yana ɗauke da watanni shida, wanda ya haɗa da lokacin karatu da na jarrabawa, gabaɗaya Diplomar za a gama ta ne a tsawon shekara ɗaya, wato watanni goma sha biyu, sannan kuma akwai ɗan taƙaitaccen hutu a tsakanin zangunan biyu.
Jarrabawa da kuma sakamako:
  • Jarrabawa ta asali:
    Ita ce jarrabawar da ake yi a ƙarshen kowace madda da aka karanta, da nufin auna fahimtar ɗalibai, da kuma auna cigaban da suka samu, kuma jarrabawar dole ce a ƙarshen kowace madda, kuma za bayar da damar a yi ta ne tsakanin kwanaki uku.
  • Jarrabawar cike giɓi:

    Ita ce jarrabawar da ɗalibai suke yi waɗanda ba su sami makin da zai ba su damar cin jarrabawa ba a jarrabawa ta asali, ko kuma ba su sami damar yin jarrabawar asali ba.

    Ana bayar da damar yin su bakiɗaya a lokaci guda bayan kammala zangon karatun jarrabawar cike gurbi ta dukkan maddojin.

     Kuma ana ba ta tsawon tazarar kwana goma ne kawai.

Maki da lissafin sakamako:
  • Kowace madda tana da maki 100.
  • Makin da zai ba wa mutum damar cin jarrabawa ta asali, da ta cike giɓi; shi ne maki 50 zuwa sama.
  • Ɗalibi ba za a yi la’akari da cin jarrabawarsa ba; har sai ya ci jarrabawar dukkanin maddojinsa.
  • Bayan kammala dukkanin manhaja; ɗalibi zai ga dukkanin makin da ya samu.
Shirye-shirye na zaburarwa:
  • Tsawon lokacin karatun akwai Shirye-shirye na zaburarwa, da kuma Gasa mai dangantaka da ilimi, da sauransu, da nufin samar da yanayin da zai zaburar da ɗalibai, ya kuma ɗebe musu kewa, ya kuma taimaka musu wajen cigaba da karatu, da kuma ƙin yanke shi.
  • Dukkanin waɗannan za su kasance ne a ƙarƙashin Shirye-shiryen zaburarwa, da kuma karatu a cikin rukunin sadarwar da aka ƙayyade don binciken.
Takardar shaida:
  • Ɗalibi yana cancantar ta ne; da zarar ya sami makin cin jarrabawa (wato maki 50) zuwa sama a dukkanin zangunan karatu guda biyu. kuma zai karɓi takardar kammala karatu ta Dijital wadda Tsangayar za ta ba shi, za a ba shi kai-tsaye ta asusunsa na shafinsa, sai ya ɗauke ta.