An buɗu yin rigistar rukuni na biyu, na Diplomar
ilumimmukan Shari’ar Musulunci.
tsarin karatu ne na Diploma, na tsawon shekara ɗaya. an raba karatun zuwa rukuni-rukuni, za a sanar da ɗaukar ɗalibai a kowane rukuni, a Tasahar Africa tv3, da kuma dandulansu na sa da zumunta tun kafin fara rijista da cikakken lokaci. Wannan Diplomar tana da zango biyu, da ɗalibi zai karanci maddoji shida a cikinsu a kowane zangon. bayan ɗalibi ya ci jarrabawar ƙarshe a kowane zango, to zai sami takardar shadar kammalawa ta Diplomar Shari’ar Musulunci, daga Tsangayar Africa.
Litattafai na PDF
Sanya karatu kai tsaye a YouTube
Laccoci na sauraro (Mp3)
Laccoci na bidiyo waɗanda za a gani a tashar Africa tv3
tsarin karatun ana yin shi ne daga nesa, ta yadda ɗalibi zai zaɓi tsarin karatun da zai dace da shi, daga cikin mabambantan tsaruka, kamar yanayin tsarin yadda ake gabatar da maddojin ta mabambantan hanyoyi, ta hanyar littafin karatu, da laccoci na bidiyo, da kuma na sauti.
ka sauke littafin jagoran ɗalibi, domin sanin komai game da tsarin karatu a wannan dandalin
Dr. Abdulƙadir Isma_il
Dr. Abubakar M. Birnin-Kudu
Shkh. AbdulMuɗɗalib Awwal Gusau
Dr. Nazifi Inuwa
Dr. Yusha_u Hanafi
Dr. Habeeb Tijjani Tahir
Shkh. AbdulMuɗɗalib Awwal Gusau
An kiyaye duk haƙƙoƙin mallaka © 2024