Tsangayar Africa ta koyar da ilimi daga nesa: Na farin cikin karɓar dukkanin ɗalibai; masu sha’awar koyon ilimin Shari’ar Musulunci, ba tare da buƙatar samun wata takardar shaida ta musamman ba.
Kawai abin da ake buƙata shi ne ya kasance ya iya harshen Hausa, ta hanyar yin magana, da rubutu, da karatu, saboda shi ne harshen da ake amfani da shi a Tsangayar Africa, wajen koyo da koyarwa.
Kuma kada shekarun ɗalibi su yi ƙasa da shekara 15.
Sannan kuma ɗalibi ya yi rijista ta yadda aka buƙata.