A wannan maddar ɗalibi zai nazarci: Ma’anar ilimin Aƙida, da bayanin matafiyar Ahlus Sunna wal jama’a game da abin da za a ƙudurce, za a gabatar da karatun ta hanya mai sauƙi, ba tare da cusa abubuwa ba, kuma ba tare da kawo abubuwan da suka saɓa wa shari’a ba, kuma ɗalibi zai san maɓuɓɓugan da ake ciro Aƙida daga cikinsu, da kuma abin da Aƙidar Musulunci ta keɓanta da shi, da kuma yin bayani game da ma’anar Tauhidi da rabe-rabensa, da kuma guraren da ake samun zamewar ƙafa a cikinsu, da kuma dasa ilimin tauhidin kaɗaitakar Allah a ibada, sannan kuma za ta ba wa ɗalibi guzurin hujjoji waɗanda zai yi amfani da su domin mayar da martani game da ruɗanin da waɗanda ba su yarda da Allah ba suke kawowa, da kuma masu rajin cewa a sake duba game da nassoshin shari’ar Musulunci, da kuma bayani game da tunani, da kuma ƙa’idojinsa, da kuma alamomin tashin ƙiyama, da kuma bayani game da Sahabbai, da kuma Ahlul baiti Allah Ya yarda da su baki ɗaya, da kuma waliyyai da karamominsu, da kuma ceto, da abubuwan da suke da dangantaka da shi.
A maddar Tafsiri za a horar da ɗalibi game da: Shimfiɗa game da ilimin Tafsiri, da kuma fassarar suratul Fatiha, da Ayatul kursi, da ayoyin ƙarshen suratul Baƙara, da kuma fassarar Juzu’in Amma bakiɗaya, tare da ambaton mafi muhimmancin fa’idojin da ayoyin suka ƙunsa, kuma a wajen wallafa littafin an dogara ne da mafi shaharar litattafan tafsiri na da can, da na yanzu.
Dalibi zai nazarci wasu zaɓaɓɓun hadisan Manzon Allah tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, waɗanda suka tattara ginshiƙan shari’a, da ginshiƙan halaye, da ladubba, da abubuwan da aka hana, waɗanda aka ciro su daga mafiya muhimmancin litattafan hadisi da kuma sharhinsu, da kuma Aƙida, da ladubba na shari’ar Musulunci.
A maddar Fiƙihu ɗalibi zai nazarci fiƙihun ibadun da suka wajaba a kan kowane musulmi ya koye su, tun daga kan tsarki, har zuwa aikin hajji. Sannan sai littafin ya tuƙe zuwa ga littafin da ya game bayanai game da ma’amalar dukiya, a taƙaice, kuma cikin sauƙi, da kuma wasu abubuwan da suke faruwa masu dangantaka da likitanci, da kuma bayani game da mas’alolin fiƙihun iyali, da kuma rantsuwa, da bakance, da kuma mas’alolin abin sha, da abinci. An kawo su ta hanya ta zamani mai ƙayatarwa, tare da haɗa su da ɗaukakkun hotuna, ya kuma bijiro da su cikin sauƙi, kuma ya dogara ne kacokan a kan manyan hujjoji, da kuma kaucewa yin amfani da kalmnomi masu wahala, da kuma saɓani.
A maddar Sira ɗalibi zai nazarci Sirar Annabi ﷺ bakiɗayanta, a taƙaice, sannan kuma zai karanci ɗabi’un Annabi ﷺ, sannan kuma zai tsaya akan wasu daga cikin abubuwa da yanayin da suka faru a rayuwar Annabi ﷺ, a mataki na ƙarshe kuma zai nazarci yanayin ma’amalar Annabi ﷺ tare da mutane a taƙaice, sannan kuma a kawo kyawawan maganganun malamai game da abin da ya gabata.
A maddar Tarbiyyar Musulunci ɗalibi zai nazarci babuka mabambanta da suke da dangantaka da wayewa ta Musulunci, waɗanda basu da dangantaka da manhajojin da suka gabata, a mataki na farko; zai karanci, haƙƙoki, waɗanda daga ciki akwai haƙƙin Allah, sannan sai haƙƙin Annabi ﷺ, sannan sai haƙƙin Sahabbai Allah Ya yarda da su, sannan sai haƙƙin iyaye, sannan sai haƙƙin miji da mata… sannan sai ya karanci ladubba na Shari’a, sannan sai ya tuƙe da nazartar cututtukan zuciya, da kuma hanyoyin kuɓuta daga alamominsu.
An kiyaye duk haƙƙoƙin mallaka © 2024